Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Majiyar Jami’an lafiya da likitoci a birnin na kunduz ta fadi cewa harin ta’addancin da kungiyar ta’adda ta Daesh ta kai a masallacin mabiyar mazhabar shi’a a garin ya haddasa mutuwar mutane 150 dare da jikkata wasu guda 200 na daban,
Ana ta bangaren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta yi Tir da wannan harin na ta’adanci da kungiyar wahabiyawa masu kafirta mutane suka kai masallaci, kana ta ce: “ya yi hannun riga da duk wani addinin da kuma hakkin dan adam. Kuma ta nuna tausayi da alhini ga iyalan wadanda suka yi shahada da kuma wadanda suka jikkata,
Har ila yau ta yi kira ga shugabannin Addini a dukkan kasashen musulmi da su dauki tsauraren matakai kan wannan danyen aikin da kungiyar Takfir ta wahabiyawa ta ke yi da mayar da ita saniyar ware, kuma ta bukaci mahukumta kasar da su hukumta wadanda suka aikata wannan mummunan ta’adancin.
342/